Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Waje Da 'Yan Wasan Flying Eagles


Anyi waje da ‘yan wasan flying Eagles a wasan su na shiga gasar cin kofin FIFA na duniya na ‘yan kasa da shekaru ashirin bayan karawar su da ‘yan wasan Jamani inda aka yi masu ci 1 – 0 a wasan su na zagaye 16.

Wannan nasarar da dan wasan Jamani Oztunali ya samu cikin minti na 19 ne kadai ‘yan wasan ke bukata domin tsallakewa zuwa shiga wasan kusa da karshe.

Kulob din na Jamus ya fara wasan ne da niyyar samun galaba akan takwarorin nasu, kuma kwatsam sai hakan ya kasance, inda suka bar ‘yan wasan na flying Eagles da kokarin tsaron gida bayan cin ada aka yi masu.

Gwagwarmayar da ‘yan wasan flying Eagles sukai tayi domin rama cin da Oztunali na Jamani yayi masu bai kai ko ina ba saboda irin rawar ganin da ‘Yan wasan na jamani suka taka, har zuwa hutun rabin lokaci.

A cigaban wasan bayan hutun rabin lokaci, ‘yan wasan na Flying Eagles da ke fama da sanyi a filin wasan Christchurch stadium, sun dawo da kwarin gwiwa amma hakan baiba ‘yan wasan na jamani tsoro ba, kamar yadda suka cigaba da wasan su kamar yadda suka fara da farko.

‘yan wasan na Flying Eagles sun cigaba da neman samun daidaitawa amma hakan ya ci tura har wasan ya kai ga karshe.

Duk da akarin lokacin da akayi masu, kokarin na ‘yan wasan Flying Eagles bai basu nasarar keta wa tsakanin ‘yan tsaron gidan na Jamani ba har zuwa tashin wasan.

XS
SM
MD
LG