Hankalin al’ummar musulmai a duniya ya karkata ne wajen shirye shiryen watan Ramadan, wato wata mai falala a daukacin watannin musulunci gomasha biyu. Yanzu haka dai a Najeriya, ba a bar mutane a baya ba, don kuwa kowa na ta wannan shirye shiryen.
Wasu da suka bayyana halin da suke ciki da kuma irin yadda suke nasu shirin, suna nuni da cewar wannan lokacine da yakamata ace ‘yan kasuwa da ma masu hannu da shuni suyi koyi da koyarwar manzon rahama da kuma sahabbansa, wanda yafi dacewa dasu saukakar da kayan masaruhi ga masu karamin karfi.
Sun dai bazama cikin kasuwanni don sayan kayyyakin da zasu bukata a wannan watan mai falala, da kuma kokarin yawaita kyauta da sadaka ga mabukata a ko ina suke, kana abun da yadace ayi a wannan watan kasancewar shi wata mai albarka, da Allah subhanahu wata’ala ke karbar addu’o’in bayinsa to lallai yazama wajibi ga kowane mahaluki ya kokarta wajen taimakama masu karamin karfi da kuma zagewa wajen ibada, da rokama kasar su addu’a da ma duniya baki daya, da Allah ya kawo zaman lafiya a ko ina, kuma Allah ya bayyanar da gaskia a ko ina take.