Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Hana a Baiwa Gwamnatocin Jihohi Bashi


Jami’an tsohuwar Gwamnatin jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, na ci gaba da maida martini kan matakin da Gwamnati mai ci yanzo ta dauka a binciko wasu kudade ga manyan jami’an Gwamnatin da ta gabata.

Tsohon sakataren Gwamnatin jihar Neja, Alhaji Idris Ndako, ya kira taron manema labarai inda yayi bayani akan wasu kudade kimanin Naira Miliyan dubu ukku, da akace sun ciwo bashi kuma sun rabawa kansu a daidai lokacin da suke daf da barin mulki.

Alhaji Idris Ndako, yace “Irin wannan bashi da akace sun karbo, kowa a Najeriya, yasan cewa tun farko wannan shekarar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya rubuta duk bankunan kasar cewa kada su baiwa kowace Gwamnati jihar bashi toh a wani banki tsohowar Gwamnatin na jihar Neja ta samo nata bashin.”

Ya kara da cewa “ Ni dai a matsayi nan a sakataren Gwamnatin jihar a lokaci da ake Magana akai duk abubuwan da za’a yi ana tattaunawa a taron majalisar zartarwa na jihar ni kuwa ban ji ba ban kuma ganin ba cewa an karbi wani kudi bashi ba.”

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello, ya shedawa manema labarai a jiya cewa ba zasu bata lokaci wajen gudanar da bincike ba amma wannan bai hana cewar idan aka gano barna a barshi ba.lallai idan aka gano wani abu za’a kira mutun domin yayi bayani.

XS
SM
MD
LG