Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kananan Yara na fuskantar Matsaloli


Yara Kanana
Yara Kanana

Yau take ranar yaki da bautar da yara kanana, Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 12 ga watan Yuni domin tunatar da duniya rashin alfanun bautar da yara kanana wanda hakan cin zarafi ne. Taken na bana, ya jawo hankali jama'a, ne dangane da harkokin ilimin kanaan yara.

Bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa, miliyoyin kananan yara ne ake tilastawa ayyukan karfi, ko bauta, ko karuwanci, wani lokaci ma harda safarar miyagun kwayoyi domin biyan bukatun iyayensu.

Duk da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka rabbata hannu a kundin kare kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, kananan yara a kasar suna fuskantar matsala kama daga aikin gida, da barace barace ,da kuma rashin karatu.

XS
SM
MD
LG