A tsarin makarantu a nan kasar Amrka, malami ko malama basu da hurumin hukunta yaro idan yayi laifi, amma suna iya korar yaro daga cikin ajin su a lokacin da ake gudanar da darasi, ko ace ana iya hukunta yaro ta dakatar dashi daga zuwa makaranta har na tsawon kwanaki, wanna na iyasa dalibi ko daliba mai hazaka su koma baya, dalili kuwa shine a lokacin da ake gudanar da darasi yara sunfi fahimtar karatu a lokacin da suke tare da abokan karatunsu, saboda gasa dake a tsakanin yara don kowa nason yazama zakara.
Wato babbar illar wanna hukuncin shine idan yaro bai je makaranta ba, a irin wannan lokacin ne sukan hadu da sauran yara ‘yan’uwansu a cikin anguwani, wanda daganan ne zasu fara aiwatar da wasu kanana kananan laifufuka wanda daga bisani basu samun damar kamala karatun sakandire.
Wanda daga garshe sukan zamo masu aiwatar da manya laifufuka da zai yi sanadiyyar zuwan su gidan kasu. Lallai wannan wani abun koma baya ne ga cigaban kasa da kuma fannin ilimi baki daya. Don haka lallai yazama wajibi a fito da wani tsarin hukuntar da dalibai wanda zai rage yawan hau-hawa lafifufuka, wannan binciken nasu yana nuni da cewar wasu jinsin mutane sunfi aiwatar da yawan laifufuka. Amma abun tambaya a nan shine aikata laifi nada alaka da irin jinsin mutun?