Jam'iyyar PDP ta kara nuna fushinta da yadda hukumar EFCC ke cigaba da tsare kakainta ba tare da gurfanar dashi gaban kotu ba.
PDPD ta bakin lauyanta Victor Kong tace ya zama wajibi gwamnatin Buhari ta mutunta hakin kakakinta Chief Olise Metuh ta hanyar gurfanar dashi gaban shari'a.
Kazalika jam'iyyar ta nuna bacin rai game da kalamun mataimakin Metu Barrister Jalo wanda yace irin su Metuh sun lashe kudaden makamai ne su hudu.
To saidai shi Metuh yana fuskantar karin tuhuma bakwai a karar da EFCC ta shigar gaban kotun tarayya, ya shafi dankawa shugaban kwamitin amintattun PDP Chief Tony Anenih nera miliyan ashirin da daya da dubu dari bakwai daga ofishin tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.
Lauyan Metuh ya shigar da kara a babban kotun tarayyar yana bukatar a tilasta EFCC ta mutunta hakokinsa na dan Adam ta hanyar barinsa ya koma gida.
Alkalin kotun ya dage sauraren karar zuwar ranar 27 ta wannan watan domin jin bahasi daga EFCC.
Amma Dattijo Husaini Gariko na ganin da zara shari'a ta shiga kotu yiwuwar hukunta masu laifi na dushewa. Yace idan ba'a gyara shari'a ba a kori duk alkalan da aka sani da karban na goro domin karkata shari'a to da wuya a samu cigaba da yaki da cin hanci da rashawa. Yakamata shugaban kasa ya dubi bangaren shari'a ya tace alkalai.
Dan PDP Lamido Umar Cikere na ganin shugaba Buhari ya mayar da hankalinsa ne akan abu daya, yaki da cin hanci da rashawa. Yakamata ya soma cika alkawura da ya yi kada lokaci ya kure masa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5