Sakamakon zaben da aka kammala ya nuna cewa gwamnan jihar Siriake Dickson na jam'iyyar PDP ne ya samu nasara.
Da bayyana sakamakon al'ummomin jihar suka fara bayyana ra'ayoyinsu. Wata matashiya tace bata ji dadin nasarar da gwamnan ya samu ba to amma Allah ne ya bashi da fatan zai taimakawa jama'ar jihar. Wani kuma murna ya yi da cewa suna da sabon gwamna da zai yi masu jagoranci na shekaru hudu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali tar da kiran gwamnan ya tallafawa matasa sosai.
Wani Alhaji Musa Saidu masani akan harkokin siyasar jihar Bayelsa yace duk wanda aka kashe sai an anbaci sunasa. Ya kuma ambaci sunan wanda shi ne umalubaisan kashe-kashen da aka yi tare da cewa duk wanda yace ba'a kashe mutane ba to bai yi adalci ba.
Duk da cewa bayanai sun sanar da salwantar rayuka cikin rigingimun da suka taso amma jami'an tsaro sun ce zaben ya gudana lafiya kuma babu wanda aka kashe. DIG Salihu Hashimu Argungu babban mataimakin sifeton 'yansandan Najeriya ya karyata batun cewa an kashe an kuma jikata mutane. Yace babu kuma wani mai bautawa kasa ko NYSC da aka kama da wani laifi. Yace duk sun bincika kuma babu gaskiya.
Ga karin bayani.