Ouattara Ya yi Kira Ga 'Yan Kasar Cote d"voire, Su Fara Yajin Gamagari

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya suke sintiri a birnin Abidjan

Mutuminda duk Duniya ta yarda shine ya lashe zaben shugaban kasa a Ivory Coast,Alassane Ouattara ya yi kira ga ‘yan kasar baki daya su fara yajin gama gari daga ranar litinin.

Mutuminda duk Duniya ta yarda shine ya lashe zaben shugaban kasa a Ivory Coast, Alassane Ouattara ya yi kira ga ‘yan kasar baki daya su fara yajin gama gari daga ranar litinin,yajin aiki day ace zai dore har sai shugaba Laurent Gbagbo ya sauka daga kan mulki.

Wani kakakin gamayyar jam’iyun dake goyon bayan Mr. Ouattara,an ji yana cewa ko kusa ba zasu bari a sace nasarar da ya samua azaben fidda gwani da aka yi cikin watan Nuwamba ba.

Kiran a fara yajin aikin yazo ne jim kadan bayan an hana jirgin shugaban kasan Laurent Gbago tashi daga tashar jiragen kasar Faransa.

Kakakin ma’aikatarr harkokin wajen faransa Bernard Valero,ya gayawa manema labarai yau lahadi cewa an hana jirgin dake daukan shugaban kasa Laurent Gabgbo tashi a tashar jiragen Basel-Mulhouse. Shugaban kasan baya cikin jirgin.

Kakakin yace “sahihan hukumomin” kasar Ivory Coast ne suka nemi a hana jirgin tashi. “Abinda kuma muka yi kenan”.Yana nufin banagaren Alassane Ouattara ne suka bukaci faransa ta yi haka.

Ana sa ran wata tawagar shugabannin kasashe daga yammacin Afirka zasu kai ziyara Abidjan cikin makon nan.

Ana kuma ci gaba da bayyana faragbar cewa cijewarda aka samu na iya sake jefa kasar cikin yakin basasa.