‘Yan takara a zagaye na biyu domin fidda gwani a zaben Ivory Coast sun hada da shugaba mai ci na yanzu Laurent Gbagbo da kuma babban abokin karawarsa Alassane Ouattara. An bada rahoton zaman dar-dar a yanayin zaben ganin yadda aka rika tashin hankali a zaben zagaye na farko. Gashi kuma a jajiberen zagaye na biyu, shugaban Gbagbo ya bada umarnin kafa dokar hana yawo tun daga ran Asabar har zuwa washegarin zaben. Shaidun gani da aido sun ce akwai wasu rumfunan zaben dake birnin Abidjan da ba’a fara jefa kuri’a ba a kan lokaci ba saboda dokar hana zirga-zirgar ta hana ma’aikatan zaben zuwa wuraren ayyukansu a kan lokaci.
Wannan zaben, zagaye na biyu shine ake ganin irinsa na farko tun shekarar 2002 lokacin da kasar Ivory Coast ke rabe, bangaren ‘yabn tawaye da bangaren dake hannun Gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo.