Rahotanni daga Najeriya na cewa ga dukkan alamu, kamfanin mai na NNPCL ya kara farashin litar man fetur.
Kafofin yada labaran kasar sun ce farashin ya tashi daga naira 568 zuwa naira 855.
Wasu rahotanni sun ce farashin litar a wasu manya biranen kasar ya kai har 925 zuwa 1,000.
Kamfanin dai bai ce uffan ba kan batun karin farashin litar man a lokacin hada wannan rahoto, amma ya yi korafi kan bashi da masu shigo da mai suke bin sa wanda ya kai kusan dala biliyan 6.
“NNPC ya ga rahotanni a jaridu kan batun bashin da masu shigo da mai suke bin sa.
“Wannan matsi na bashi na matukar takura kamfanin yana kuma barazana ga dorewar samar da man.” Wata sanarwa da Kakakin kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar lahadi ta ce.
Sama da makonni uku da suka gabata ake ta fama da matsalar karancin man a sassan kasar lamarin da ke haifar da dogayen layukan motoci a gidajen mai.