Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanfanin Mai Na Najeriya NNPC Na Fuskantar Matsalolin Kudi


Malam Mele Kyari Shugaban NNPC, Najeriya
Malam Mele Kyari Shugaban NNPC, Najeriya

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya tabbatar da cewa ya na fuskantar matsalar kudi sakamakon tsadar man fetur na manyan injuna (PMS), lamarin da ke kawo cikas ga dorewar ayyukan samar da man.

Babban jami’in shashen sadarwar Kamfanin man na NNPC, Mr. Olufemi Soneye shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ga manema labarai a ranar Lahadi 1 ga watan Satumba.

Sanarwar ta ce: "NNPC na fuskantar matsalar karancin kudi saboda farashin kayan sarrafa man PMS, lamarin da ke tasiri ga dorewar raba man."

Kamfanin NNPC ya tabbatar da rahotannin baya bayan nan da aka buga a jaridun kasar game da dimbin basussukan da kamfanin ke bin masu samar da mai.

Ya ce wannan matsalar kudi ta sanya matsin lamba sosai kan Kamfanin tare da yin barazana ga dorewar samar da mai.:47

Kamfanin man na kasa ya ce bisa ga dokar masana'antar man fetur, ya ci gaba da sadaukar da kai ga matsayinsa na mai samar da mafita ta karshe, wajen tabbatar da samar da makamashi a kasar.

Kamfanin ya ce: "Muna hada kai da hukumomin gwamnati da suka dace da sauran masu ruwa da tsaki don ci gaba da samar da albarkatun mai a fadin kasar."

-The Nation-

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG