Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dillalan Man Fetur A Arewacin Najeriya Sun Koka Kan Sabon Haraji Da Zai Kuntata Wa Talaka


Wani gidan mai a Najeriya
Wani gidan mai a Najeriya

A yayin da ‘yan Nigeria ke ci gaba da fuskantar tsadar man fetur, a yanzu haka wata sabuwar cuwa-cuwa ta bullo a cibiyoyin sayo man da ke biranen Legas, Wari da kuma Fatakwal.

Manyan dillalan da ke sayo man zuwa arewacin Nigeria sun koka a kan wani sabon harajin da baya da tushe da Kungiyar Direbobin Tanka Masu Dakon Man ke karba a kan ko wacce litar man fetur guda.

Shugaban kamfanin mai na Fist Al-Shabba Nigeria Limited, Alh. Abdullahi Sarkin Turke ya ce yanzu haka ba su da damar dauko mai sai sun biya Naira daya a kan ko wace litar mai da motar tanka za ta dauka.

Alh. Babangida da Bashir Muhammada Ruwanzafi, wakilai ne na kamfanonin sayar da mai a arewacin Nigeria da suke zaune a Legas da Wari sun bukaci ganin Gwamnati ta shiga cikin lamarin domin kawo karshen shi bisa lura da yadda lamarin ke karewa a kan talakawan kasa.

Sai dai a zantawa ta wayar salula, mataimakin shugaban Kungiyar Direbobin Tankar a Nigeria, Malam Abubakar Malu ya ce ba su da masaniya a kan wannan sabon haraji amma za su gudanar da bincike a kan lamarin.

A halin yanzu dai ana sayar da litar mai fetur daga Naira dari tara zuwa dubu daya a kusan dukkanin jihohin Arewacin Nigeria, sabanin Naira dari shidda da Naira goma sha bakwai da Gwamnatin Najeriyar ta ce a sayar.

Ga sautin rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna:

Dillalan Man Fetur A Arewacin Najeriya Sun Koka Kan Sabon Haraji Da Zai Kuntata Wa Talaka.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG