Rahotanni na cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wata bukata da kamfanin mai na kasa na NNPCL ya mika masa na yin amfani da ribar da aka samu ta shekarar 2023 don biyan tallafin mai.
Jaridar yanar gizo ta The Cable ce ta ruwaito a ranar Litinin.
Hukumomin Najeriya sun sha musanta cewa an dawo da tallafin man duk da wasu rahotanni da suka nuna cewa gwamnati na biyan kudaden ta bayan fage.
The Cable ta ruwaito cewa hasashen kamfanin na NNPCL da ta gani, ya nuna cewa jimullar kudin tallafin mai da za a kashe daga watan Agustan bara zai kai naira biliyan 6.884 nan da zuwa watan Disambar 2024.
A watan Mayun shekarar 2023 bayan karbar rantsuwar kama aiki, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai lamarin da ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki.
A zanga-zangar da wasu ‘yan Najeriya suka yi a farkon watan nan, neman mayar da tallafin man na daga cikin jerin bukatun da masu boren suka zayyana.
Sai dai ko a jawabin da ya yi ga kasa a lokacin ana ganiyar zanga-zangar, Tinubu ya nuna cewa ba za a dawo da tallafin man ba.
Gwamnatin ta Tinubu ta ce ta yi nasarar tara tiriliyoyin naira sanadiyyar cire tallafin man wanda ta ce wasu tsirarun masu hannu da shuni ne suke amfana.
Tun bayan cire tallafin man, litar fetur ta tashi a gidajen mai lamarin da ya harbi sauran fannonin hada-hadar kudaden dagan bisani ya jefa jama’a cikin kangin tsadar rayuwa.
Wasu masana da masu lura da al'amura na cewa ko da an dawo da tallafin na mai ba a ganin tasirinsa kamar a baya duba da yadda ake samun hauhawar farashin kayayyaki.
Dandalin Mu Tattauna