Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Gano Hanyoyin Da Ake Satar Man Fetur A Najeriya – NNPC


Shugaban NNPCL, Mele Kyari
Shugaban NNPCL, Mele Kyari

lamarin na faruwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan batun tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta cire a bara, amma kuma wasu rahotanni ke zargin ana ci gaba da biyan kudin ta bayan fage.

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, ya ce ya gano karin wasu hanyoyi da ake satar danyen man fetur a kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a shafukan sada zumunta, NNPC ya ce ya gano wasu hayoyin bututan mai 33 da haramtattun matatun man fetur 220.

“Cikin mako guda mun gano haramtattun hanyoyi 33 na bututun mai da haramtattun matatun man fetur 220.” Sanarwar mai taken ‘Yaki da satar danyen man fetur’ ta ce.

Wannan sanarwa da kamfanin na NNPC ya fitar na zuwa kwana guda bayan da ya ayyana samun ribar naira tiriliyan 3.3 a shekarar 2023.

Kazalika lamarin na faruwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan batun tallafin man fetur da gwamnati Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta cire a bara, amma kuma wasu rahotanni ke zargin ana ci gaba da biyan kudin ta bayan fage.

Shi dai kamfanin na NNPC ya ce kudaden da ake ikirarin an biya ba na tallafin mai ba ne duk da rahoton da jaridar yanar gizo ta The Cable ta ruwaito da ke cewa Tinubu ya ba kamfanin na NNPC umarnin ya biya wasu kudade a matsayin na tallafin man fetur.

A lokacin hada wannan rahoto, ana kuma fama da matsalar karancin man na fetur inda ake ganin dogayen layukan motoci a gidajen mai a manyan biranen kasar.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a ranar Litinin ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta fito ta fayyace wa ‘yan Najeriya takaddamar biyan kudin na tallafin mai yana mai cewa lamarin ya jefa al’umar kasar cikin rudani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG