Nijer Da Najeriya Da Aljeriya Sun Saka Hannu Kan Yarjejeniyar Farfado Da Ayyukan Shimfida Bututun Iskar Gaz

Bututun mai.

Jamhuriyar Nijer, Najeriya da Algeria sun rattaba hannu akan yarjejeniyar farfado da aiyukan shimfida bututun iskar Gaz daga Najeriya zuwa Aljeriya ratsawa ta Nijer da nufin sayarda iskar gaz a kasuwanin kasashen nahiyar turai.

Yayinda abin zai kuma zama wata hanya ce ta samarda kudaden shiga ga al’umomin garuruwan da bututun zai ratsa.

Ministan man fetur da makamashi na jamhuriyar Nijer Mahaman Sani Mahamadou sun rattaba hannu da takwarorinsa na Najeriya da na Aljeriya akan takardun yarjejeniyar farfado da ayyukan shimfida bututun iskar Gaz din da zai ratsa kasashen 3 bayan da aka jingine wannan aiki a shekarun da suka gabata a bisa wasu dalilai.

Mahimmancin wannan kudiri ya sa gwamnatocin Nijer da Najeriya da Aljeriya sake jan damara domin tabbatuwar wannan dadaden mafarki na fara cin kasuwanin nahiyar turai.

Dr Umar Faruk Ibrahim shine babban sakataren kungiyar kasashen Afrika masu arzikin mai da ma’adanai. "Wato an dade ana yi, ya fi shakara 20 da wani abu, sai aje a dawo-aje a dawo, abun na taffiyan hawaniya, amma da alama yanzu shuwagababnin sun maida hankali akai, har sun sa hannu, fata shine daga nan za a cigaba."

Ministan albarkatun man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya jaddada cewa kasar ba za ta yi sanyi ba wajen ganin wannan aiki ya kankama.

Yace “daga yanzu zamu yi duk iya kokarinmu donganin mun shimfida bututun da zai isa Kano daga nan ya kai bakin iyakar mu. In ya so kuma bututun na transaharien Gazoduc daga Kano zai kama hanya zuwa gaba.”

An dai bayyana cewa idan aka kammala wannan aiki al’umomin yankunan da bututun zai ratsa zasu amfana da abubuwa da dama.

A watan gobe tawagogin ministocin kasashen zasu hadu a Abuja domin ci gaba da tantauwa akan wannan gagarumin aiki dake bukatar hadin kan wadanan kasashen 3.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumini Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijer Da Najeriya Da Aljeriya Sun Saka Hannu Kan Yarjejeniyar Farfado Da Ayyukan Shimfida Bututun Iskar Gaz