Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Wanke Kamfanin Shell a Badakalar Sayen Filin Tona Mai A Najeriya


A wannan makon, wata kotun Italiya da ke Milan ta wanke babban kamfanin mai da iskar gas na Italiya Eni da kuma Kamfanin Mai na Shell daga zargin cin hanci da rashawa dangane da sayen filin mai a Najeriya.

A cewar kungiyar Global Witness, an gurfanar da kamfanonin biyu ne tun a shekarar 2018 a lokacin da su ka sayi wani filin mai na Najeriya a shekarar 2011.

Sun biya dala biliyan 1.3 don samun lasisin tona filin. Dala biliyan 1.1 daga cikin kudin za a biya kamfanin Malabu Oil and Gas, kamfanin da ke karkashin kulawar Ministan Mai na Nijeriya a lokacin, Dan Etete.

A zahiri, Etete ya bai wa kamfanin nasa lasisi yayin da yake cikin gwamnati.

Barnaby Pace, wani babban dan gwagwarmaya a kungiyar ta Global Witness, ya fadawa wakilin Muryar Amurka James Butty cewa kungiyoyi masu zaman kansu da masu fafutuka sun ji takaici da kuma fusata game da wanke manyan kamfanonin biyu masu gurbata muhalli a duniya.

Ya ce kungiyoyin sun kuma bukaci ofishin mai gabatar da kara na Milan da ya yi la’akari da daukaka kara kan hukuncin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG