Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaso 3 Ya Mana Kadan, In Ji Yankunan Da Ake Hako Arzikin Man Najeriya


Kungiyoyin kudancin Najeriya daga jihohin Abia, Delta, Edo, Ondo sun bukaci gwamnati da ‘yan masalisun dokoki su sake nazarin yin kari kan matsayar ba da kashi 3 cikin 100 na albarkatun man da ake hakowa domin raya yankunansu.

Martanin kungiyoyin yankunan da ake hakar danyen mai a cikin su na zuwa ne bayan zartar da kudurin bangaren kasuwancin man fetur wato PIB zuwa doka a ranar alhamis da ta gabata.

Lamarin dai ya cigaba da samun mabanbantan ra’ayoyi daga ‘yan kudancin kasar.

Duk da cewa, sashi na 240 na daftarin kudurin ya gabatar da kaso 5 ne cikin 100 na ribar da kamfanonin mai ke samu a duk shekara ga al'ummomin yankunan da ake hakar mai a cikin su, ’yan majalisar dattawa sun rage kason na asusun da aka ware wa al’umman yankunan zuwa 3 cikin 100, jim kadan kafin zartar da kudurin zuwa doka.

A karshen makon da ta gabata a yayin hira da jaridar ThisDay, shugaban kungiyar masu fafutuka ci gaban ‘yan kabilar Urhobo, Cif Moses Taiga, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a wannan al’amari da su duba batun da idon basira, cikin gaskiya da kishin kasa, su kuma amince da kason asusun raya yankunansu zuwa kaso 10 cikin 100.

Cif Moses Taiga kuma bayyana cewa duk da cewa akwai gazawa a bangaren masu ruwa da tsaki kan wannan lamari, zartar da kudirin PIB zuwa doka hanya ce mai kyau kuma mai amfani wajen sauya tsarin mulki, tsare-tsare a bangare kasafin kudi na bangaren masana’antar mai da iskar gas.

Haka kuma ya yaba da kokarin yan majalisun dokoki na tarayyar kasar musamman wadanda suka fito daga yankin Neja Delta, na tabbatar da zartar da kudurin PIB zuwa doka.

A wani bangare kuwa, sakataren kungiyar yan yankin Warri wato WCF, Amaechi Ogbonna, gargadi ya yi cewa kaso 3 cikin 100 na raya kasashen su da Majalisar dattawa ta amince da su ga al'ummomin da ake hakar danyen mai a cikinsu na iya haifar da rikicin kabilanci a yankin Neja Delta.

Shi ma tsohon mataimakin babban sufeta janar na yan sanda mai ritaya, kuma shugaba al’umma a jihar Akwa-Ibom, Udom Udo Ekpoudom, ya bayyana takaici kan kaso 3 da majalisun kasar suka cimma yana mai cewa, ba su yi adalci ga yankunan da ake hakar mai a cikin su ba.

A ranar Alhamis ne majalisar dattawa ta zartar da kudirin PIB zuwa doka bayan yin dogon nazari kan duk shawarwarin da rahoton kwamitin hadin gwiwa kan bangaren hako albarkatun man fetur da bangaren sarrafawa na majalisar dattawa da na wakilai da kuma iskar gas a kan kudurin na PIB.

XS
SM
MD
LG