Dokar ta kwashi kusan shekara 20 ana kai komo a kanta kafin a kai wannan lokaci da aka amince da ita har ta zama doka.
A wata hira ta musamman da ya yi da wakiliyar Sashen Hausa Medina Dauda a Abuja, shugaban ma'aikatar man fetur ta kasa Mele Kolo Kyari ya ce wannan shi ne karon farko cikin shekara 54 da aka yi irin wannan dokar da za ta sauya halin talauci, da rashi da ‘yan kasa ke fama da shi ta hanyar mallaka masu kamfanin man fetur na kasa, wanda shi ne hanya mafi girma da ke kawo wa kasar kudaden shiga.
Mele Kolo Kyari ya ce ya yaba da matakin da shugaban kasa Mohammadu Buhari ya dauka na rattaba hannu a dokar masana'antar man fetur bayan ta kwashi shekara 20 ana gwagwarmayar tabbatar da ita.
Wannan doka dai za ta samar da tsari na gudanarwa mai kyau ga masana'antar tare da ci gaban al'umomin da ke zaune a yakunan masu arzikin mai da abubuwa da suka danganci hakan.
Kolo ya ce wannan dokar, doka ce da ya kamata kowa ya yaba domin ta sauya abubuwa da dama da aka yi shekara 54 ana yin su a harkar man fetur a kasar, kuma wannan ya zama wani abu da za a iya cewa gagarumin nasara ce ga mulkin Shugaba Mohammadu Buhari.
Kolo ya kara jadadda muhimamncin dokar ga yadda al'uman kasa za su samu abubuwan more rayuwa cikin sauki irin su wutar lantarki da iskar gas wacce za a samar da ita da dama.
Baya ga haka Kolo Kyari ya ce dubbanin matasan kasar za su samu ayyukan yi sosai kuma haka zai rage matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.
Ya kuma kara da cewa kafin yanzu, ba a samun masu zuba hannun jari a masana'antar saboda babu tabbas a harkokin mai da iskar gas amma inda ya ce yana da tabbacin wannan mataki zai sauya firgitar da ‘yan kasuwa ke yi nan ba da jimawa ba.
Idan ba a manta ba Majalisar Dattawa ta amince da dokar ranar 15 ga watan Yuli yayin da majalisar wakilai kuma ta amince da ita ranar 16 ga watan Yuli, don haka ya kawo karshen dogon jira da aka yi, duk da takkadamar da aka yi ta yi akan kason da Majalisun biyu suka ce a ba al'umomin da ke yankunan Man fetur.
Majalisar Dattawa ta ba su kashi uku cikin dari na kaso da aka amince akai amma Majalisar Wakilai kuma ta ba su kashi biyar cikin dari.
A halin yanzu dai manazarta sun ce amincewa da dokar a wanan shekarar yana da muhimmanci kwarai don jawo hankalin masu zuba jari musamman a fanin iskar gas da ragowar burbushin Man fetur.
Saurari yadda hirar tasu ta kasance: