Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin NNPC, CMEC Sun Rattaba Hannu Kan Kwantiragin Samar Da Wutar Lantarki A Maiduguri


Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

Kmfanin man fetur na Najeriya NNPC ya dauki wani mahimmin mataki na cika alkawarin ba da gudunmawarsa wajen magance matsalar rashin wutar lantarki da aka dade ana fama da shi a babban birnin Maiduguri a jihar Barno.

An rattaba hunnu akan yarjejeniyyar kwantaragin masanan da zasu sayo tare da kera na’urorin da ake bukata wajen samar da wutan lantarki na gaggawa mai karfin megawatt MW 50.

A wata sanarwar da Babban Manaja mai kula da sashin hulda da jamma’a na kamfanin Mallam Garba Deen Muhammad ya fitar, ya ce wannan matakin na daga cikin shirin NNPC na fadada amfani da iskar gas domin bunkatasa tattalin arzikin Najeriya.

Haka kuma an baiwa kamfanin China Machinery Company (CMEC) aikin sayo kayan kera na’urorin da ake bukata (EPC), yayin da kamfanin General Electric (GE) kuma zai kera na’urorin.

Da yake bayanin a wani taro da akayi don sanya hannu a kwantaragin wanda aka yi ta kafar sadarwar yanar gizo, shugaban NNPC mallam Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa sashin kamfanin mai kula da harkokin jarin iskar Gas da makamashi ne ya yanke shawarar kawo dauki a Maiduguri, ta yadda za'a yi amfani da iskar gas a matsayin wata harkar kasuwanci.

Ya kara da cewa, a matsayinsa na kamfanin mai na kasa mai yunkurin inganta al’amura, NNPC na da burin inganta samar da wadataccen wutar lantarki ga ‘yan Najeriya ta hanyar bunkasa harkar samar da wutar lantarki da isakar gas tare da na garjiya ta yadda za a samu akalla karin gigawatt 5 na wuta a kasar.

Saboda haka yace NNPC na neman hadin kan duk masu ruwa da tsaki akan wannan al’amari musamman ma kamfanonin GE da na CMEC domin tabbatar da cewar an kamala kashin aikin na farko akan lokacin da aka kayyade zuwa watan Dizamba na wannan shekara, sannan kashi na biyun kuma a hade a kammala zuwa farkon rubu'in shekara ta 2022.

Da yake mai da martini, mataimakin shugaban kamfanin GE a nahiyar Afirka da nahiyar Turai, Raisin Brice, ya bayyana cewa kamfanin yana farin cikin aiki tare da NNPC domin ganin an cimma nasarar wannan aikin a Maiduguri, kana ya ce GE zai yi amfani da kwarewarsa a kasar domin aiwatar da aikin.

Shugaban kamfanin CMEC wato kamfanin da zai aiwatar da ainihin aikin, Fang Yanshui, ya ba da tabbacin goyon baya da jajirciwa kamar takwararsa na CE.

XS
SM
MD
LG