Nijar Ta Goyi Bayan Mali Wajen Yanke Huldar Diflomasiyya Da Ukraine

Sugaban kasar Nijar

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yanke huldar diflomasiyya da Ukraine saboda kalaman da jami'ai suka ce sun nuna goyon bayan Ukraine ga kungiyoyin da ke fada a makwabciyarta Mali da suka kashe sojoji da dama da mayakan Wagner na Rasha a watan Yuli.

Nijar ta ba da sanarwar yanke huldar diflomasiya da Ukraine ne da nufin nuna goyon baya wa Mali wace ke zargin hukumomin Kiev da hada kai da mutanen da ta kira ’yan ta’adda a yayin kazamin fadan da ya yi sanadin mutuwar dimbin sojojin Mali da na Wagner a kauyen Tinzaouaten kusa da iyakar Aljeriya

Wagner

Gwamnatin mulkin sojan Nijar a sanarwar da kakakin CNSP Kanal Abdourahamane Amadou ya karanto ta fara ne da bayyana takaici dangane da munanan kalaman da kakakin ma’aikatar tattara bayanan sirrin Ukraine ya furta da wadanda jakadan Ukraine a Senegal ya yi don jaddada goyon bayan kasarsu ga hadin guiwar kungiyoyin ta’addancin da suka afkawa sojojin Mali a kauyen Tinzaouaten, abin da Nijar ke ganin ya saba wa dokokin Majalisar Dinkin Duniya da ‘yancin kasa da kasa.

Mali

Ya ce domin bai wa gwamnatin Mali da al’ummar kasar cikakken goyon baya dangane da yarjejeniyar Vienna ta 1961 wacce ta tsara sha’anin diflomasiya da kuma yarjejeniyar da ta kafa kwancen Confederation AES gwamnatin Nijar ta yanke shawarar tsinke hulda da Ukraine sannan ta kudiri aniyar shigar da kara a gaban kwamitin sulhu na MDD donganin an dauki mataki kan tursasawar da Mali ta fuskanta daga Ukraine da masu gidanta.

Matakin dai ya biyo bayan matakin da kasar Mali ta dauka ne a ranar Lahadin da ta gabata na yanke hulda da Kyiv biyo bayan kalaman da hukumar leken asiri ta sojin Ukraine ta yi game da fadan da ake yi a arewacin kasar Mali inda 'yan tawayen Abzinawa suka ce sun kashe akalla sojojin haya 84 na Wagner da sojojin Mali 47.

Russia Wagner

Lamarin dai da alama shi ne karo na farko da Wagner ta sha kashi tun bayan da ta shiga shekaru biyu da suka gabata domin taimakawa hukumomin sojin Mali wajen yakar kungiyoyin 'yan tawaye.

Tun a ranar Litinin Ukraine dai ta yi Allah wadai da matakin da Mali ta dauka na yanke huldar da ke tsakaninta da kasar a matsayin gajeriyar hangen nesa da gaggawa, Kyiv tana mai cewa ta yi watsi da zargin Ukraine tana goyon bayan ta'addancin kasa da kasa.

Takaddamar dai ta samo asali ne daga kalaman da Andriy Yusov, kakakin hukumar leken asirin sojin Ukraine ya yi a gidan telebijin, inda ya ce 'yan tawayen Mali sun samu bayanan da ake bukata domin kai harin.

MALI

Dalili kenan kwararre kan sha’anin diflomasiya Moustapha Abdoulaye ke cewa bai yi mamakin abinda ke faruwa ba a halin yanzu.

A washegarin kafsawar Tinzaouaten ‘yan awaren kungiyar CSP sun dauki alhakin wannan al’amari a yayinda hukumomin Mali ke fassara abin da aika aikar ‘yan ta’adda masu goyon bayan wasu kasashen waje matsalar da idan ba a yi hattara ba ka iya mayar da yankin Sahel tamkar wani fagen yakin Rasha da Ukraine inji masanin kan sha’anin tsaro Abass Moumouni.

Gwamnatin mulkin sojan ta Nijar dai a wannan sanarwa ta kara da cewa ba ta ji dadin yadda kasashen Afrika da kungiyar tarayyar Afrika suka yi gum da baki ba suna kallon manyan kasashen duniya a yunkurin mayar da yankin Sahel tamkar wani wurin da ‘yan ta’adda ke da damar cin karensu ba babbaka.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Goyi Bayan Mali Wajen Yanke Huldar Diflomasiyya Da Ukraine