Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Hayan Wagner Sun Ce Sun Tafka Asara A Wani Fada A Iyakar Mali Da Algeria


Mali
Mali

Sojojin hayan kungiyar Wagner ta kasar Rasha ta fada a ranar Litinin cewa mayakanta da sojojin Mali sun yi asara a wani kazamin fada da 'yan tawayen Abzinawa suka yi a kusa da kan iyakar Mali da Aljeriya.

Kasar Mali, inda hukumomin soji suka kwace mulki a wani juyin mulki a shekarar 2020 da 2021, na fama da tashe-tashen hankula na masu kishin Islama na tsawon shekaru.

Ta ce sojojin na Rasha ba sojojin haya na Wagner ba ne, amma masu horar da sojoji ne da ke taimaka wa sojojin cikin gida da kayan aiki da aka sayo daga Rasha.

Mail-Russia-Wagner
Mail-Russia-Wagner

Kungiyar 'yan tawayen, mai suna Permanent Strategic Framework for Peace, Security and Development (CSP-PSD), ta fada a ranar Asabar cewa, ta kwace motoci sulke, da manyan motoci da tankokin yaki a yakin da aka yi a garin Tinzaouaten da ke kan iyaka.

Wagner ta ce "a ranar farko, kungiyar 'Pond group' ta lalata yawancin masu kishin Islama tare da sanya sauran tserewa," in ji Wagner a Telegram.

"Duk da haka, wata guguwar rairayi da ta biyo baya ta bai wa masu tsattsauran ra'ayi damar sake hada kai tare da kara yawansu zuwa mutane 1,000.

Wagner ta ce mayakanta sun sake kare wani harin da aka kai musu amma a karkashin wata gagarumar wuta da 'yan tawaye suka yi, an samu asarar rayuka a tsakanin Wagner da sojojin Mali.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG