Nijar: Mazauna Yankin Diffa Na Korafi Kan Rashin Aikin Yi Bayan Da Al'amuran Tsaro Suka Inganta

Wasu daga cikin mazauna yankin Diffa

Harakoki sun fara dawowa sannu a hankali a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar inda jama'ar yankin ta fara komawa kan ayyukan yau da kullum bayan da aka fara shawo kan matsalar tsaron da aka yi fama da ita a shekarun baya.

Sai dai matasa na ci gaba da kiraye-kirayen ganin an samar masu aikin yi don kare su daga fadawa tarkon kungiyoyi ta’addanci da ‘yan fashi.

A kewayen babbar kasuwar Diffa wayo Marche central wacce ke ci a kowace ranar Talata wannan makon ma 29 ga watan Yuni kasuwar ta cika sosai inda masu saye da sayarwa ke harkoki ba tare da wata fargaba ba sabanin yadda abin yake a shekarun baya.

Yadda aka rika mayar da 'yan gudun hijira gidajensu a Diffa

Oumara Boulama wani matashi da ke saida katin caji a bakin kasuwa, ya ce sai dai rashin aikin yi na zama wata matsalar dake damun matasa a jihar ta Diffa duk kuwa da cewa galibinsu sun mallakin takardun shaidar kammala karatu.

A babbar tashar shiga motocin jigila na gab da babbar kasuwa mun zanta da Baba Ali shugaban ‘yan kamishon layin Diffa zuwa Gaidam inda ya ce a nan ma matasa na korafi akan rashin samun cikakkiyar damar samun ayyukan yi.

Jihar Diffa mai iyaka da jihohin Borno da Yobe a Najeriya, ta bangaren kudu na da iyaka guda da kasar Chadi ta bangaren gabashin Jamhuriyar Nijar.

Yankin na da kabilu mabambanta wadanda suka hada da Kanuri, Tubawa, Hausawa, Larabawa da Fulani.

Yadda harkokin kasuwanci suka dawo a Diffa

Galibinsu na dogara da noma da kiwo da kasuwancin kifi, sai dai matsalar tsaron da aka yi fama da ita daga 2015 zuwa 2021 ta haddasa durkushewar tattalin arzikin yankin wanda kuma sannu a hankali ke kokarin murmurewa a dalilin wasu matakan da hukumomin Nijar suka dauka a ‘yan makwanin nan.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Mazauna Yankin Diffa Na Korafi Kan Rashin Aikin Yi Bayan Da Al'amuran Tsaro Suka Inganta