Galibin ‘yan gudun hijirar dake zaune a wannan sansani na kewayen garin Diffa mata ne da yara kanana a fili suke bayyana farin cikin wannan rana ta komawa gida.
Wannan shiri na gudana a daidai lokacin da hukumomi suka fara daukan matakan sake bude kasuwanin kifi da ya zama babbar hanyar samun kudaden shiga a yankin.
Batun tsaro na da mahimmanci wajen dorewar aiyukan farfado da tattalin arzikin jihar saboda haka hukumomin Nijer suka dage akan wannan fanni inji Boube Warzagan Adamou kantoman karamar hukumar Diffa.
A tsakiyar watan nan na yuni ne hukumomin Nijer suka kaddamar da ayyukan mayar da ‘yan gudun hijirar cikin gida zuwa garuruwan da suka fito inda tuni aka kwashe sama da 5000 zuwa garin Baroua shirin da za a ci gaba da gudanarwa.
Mutane kusan 300 000 suka tserewa hare haren Boko Haram yau shekaru kusan 6 abinda ya sa shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya kudiri aniyar kai ziyara a jihar Diffa a cikin wannan mako.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: