A baya-bayan nan dakarun rundunar sun fatattaki ‘yan ta’addan Boko Haram da dama tare da karbe masu motoci da makaman yaki lokacin da suka kai farmaki a yankin Diffa lamarin da masana sha’anin tsaro ke alakantawa da wasu dabarun yaki da aka bullo da su.
Kimanin motoci kirar Pick up 15 ne dauke da mayakan Boko Haram aka bayyana cewa sun kai hari a garin Diffa a yammacin Juma’ar da ta gabata.
Sai dai wadanan maharan ba su ji dadin gamin ba sakamakon luguden wutar da suka sha ta sama da kasa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda da dama tare da kwace makamai da motoci.
Haka kuma yunkuri na biyu da ‘yan ta’adda suka yi a washe garin faruwar wannan gumurzu ya gaza yin nasara.
Yankin Diffa dake makwaftaka da jihohin Borno da Yobe a Najeriya, ya fada cikin yanayin tabarbarewar tsaro a shekarar 2015 lamarin da ya haddasa tsayawar harakokin yau da kullum.
Amma a cewar dan majalisa mai wakiltar al’umar ta Diffa Boulou Mamadou, abubuwan da suka faru a shekaranjiya na baiwa talakawa kwarin gwiwa akan yiyuwar maido da zaman lafiya a wannan yanki.
Karin bayani akan: Boko Haram, Borno, CAPAAN, Nijer, Chadi, Nigeria, da Najeriya.
Haka dai su ma ‘yan rajin kare hakkin jama’a irinsu Almansour Mohamed na kungiyar CAPAAN, sun yabawa yunkurin na sojojin Nijar da takwarorinsusu na hadin gwiwa suna masu fatan ganin an dore a haka.
Sai dai duk da galabar da dakarun gwamnati suka samu a wannan fafatawa ta garin Diffa, sanarwar sashe na 4 na rundunar hadin gwiwar kasashen Tafkin Chadi, ta ce jami’an tsaro hudu da fararen hula sun rasu yayin da wasu 14 suka ji rauni.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: