Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai A Gidan Kakakin Majalisar Dokokin Nijar


Gidan Kakakin majalisar dokokin Nijar da aka kai hari
Gidan Kakakin majalisar dokokin Nijar da aka kai hari

A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan kasar  sun fara maida martani bayan kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a gidan kakakin majalisar dokokin kasar Seyni Oumarou dake birnin Yamai a ranar Asabar 12 ga watan Yuni.

Ta hanyar wata sanawar da ta ruwaito a shafinta na yanar gizo ne kungiyar IS ko kuma Etat Islamique a faransance ta yi ikirarin cewa ta dauki alhakin harin da aka kai a gidan kakakin.

Bayyanar wannan labari a wani lokacin da ake jiran jin abinda sakamakon binciken‘yan sanda zai bayar, wani abu ne da ya fara jan hankalin masana sha’anin tsaro.

Abin tuni maharan wadanda aka bayyana cewa su biyu suka zo akan babur suka bude wuta akan jami’an tsaron dake kofar gidan na Alhaji Seyni Oumarou abinda ya ba su damar kashe mutum daya kuma suka jikkata daya kafin su arce cikin duhu.

Alakanta wannan al’amari da ta’addanci wani abu ne da ya haifar da mahawara a tsakanin jama’a yayin da wasu ke cewa akwai kamshin gaskiya wasu kuma na ganin abin tamkar yunkurin haddasa rudani ne.

Kawo yanzu hukumomi ba su maida martani akan ikirarin na kungiyar IS ba to amma wata sanarwar ma’aikatar cikin gida a washe-garin kai wannan hari ta dan kwatanta abin a matsayin wanda ya yi kama da aika-aikar ‘yan ta’adda a yayin da a wancan lokaci wasu shaidu suka ce maharan sun yi yunkurin sace wato motar jami’an tsaro dake ajiye a kofar gidan da abin ya faru .

Mafari kenan aka yi hasashen cewa barayi ne suka yi yunkurin gwada sa’arsu saboda haka rahoton binciken’yan sanda kadai ne zai fayyace zahirin abubuwan da suka wakana a cikin daren Juma’a wayewar Asabar 12 ga watan Yuni.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai A Gidan Kakakin Majalisar Dokokin Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


XS
SM
MD
LG