A karshen wani taron nazarin wannan bukata ta gurfanar da shugaba ISUHU MAHAMADU ne kwamitin gudanarwar majalisar dokokin kasar ya gano rashin dacewar hanyoyin da ‘yan adawa suka bi a yayin ajiye takardar a gabanmajalisar sakamakon lura da cewa yunkurin na ‘yan hamayyar ya sabawakundin tsarin mulkin kasa da ka’idodin majalisar kamar yadda dan majalisar dokokin kasa na bangaran rinjaye ALHAJI SHAFI’U MAGARYA ya min bayani. Ya kara da cewa ana barin halak da kunya.
Sai dai a ra’ayin ‘yan adawa masu rinjaye anfani ne suka yi da karfin mulki domin watsi da wannan bukata ta ladabtar da shugaban kasa inji TIJANI ABDUKADRI jagoran ‘yan majalisa na ARN.
A dai wani bangaren wata kotun Yamai ta sallami mutanen da aka kama a ranar da tsohon kakakin majalisar dokokin kasa Hamma Amadu ya dawo Nijar in ban da wasu kusoshin jam’iyar Moden Lumana su 4 da aka aika gidan yarin dake yammacin birnin Yamai cikinsu har da SUMANA SANDA bisa zarginsu da laifin furta kalaman da ka iya tunzura jama’a.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5