A takardar da suka shigar a ofishin shugaban majalisar dokokin kasar Nijer a yammacin Laraba ‘yan adawa na zagin shugaban kasa ISUHU MAHAMADU da rufe ido akan wasu manyan laifuka a kalla guda uku saboda haka suka ce ya sabawa rantsuwar da ya yi a gaban ‘yan kasa kan cewar zai kare dokokin jamhuriyar ko ta halin kaka.
Dan majalisar dokokin kasa a karkashin tutar jam’iyar MNSD NASARA TIJANI ABDULKADRI na daga cikin wadanda suke jagoran wannan yunkuri.
Tuni jam’iyar PNDS TARAYYA mai mulki ta soma kare shugabandaga wannan zargi wanda dan majalisar dokokin kasa ASUMANA MALAN ISA ke gani ba zasu yadda ‘yan adawa su cimma burinsu ba.
Dangata na kara tsami tsakanin bangarorin siyasar nijera yayinda kasar ke shirin gudanar da zaben gama gari a farkon shekarar 2016 kuma alamu na nuni cewa da wuya bangarorin su sasanta da juna ganin yadda hatta taron majalisar sasanta ‘yan siyasa wato CNDP ya gaza kawo karshe takun sakar dake tsakanin adawa da masu rinjaye.
Ga karin bayani.