Wata kotun birnin Yamai ta bayyana hukuncin da ta yanke a dangane da shara’ar da ta yiwa wasu dalibai kimanin 31 da aka garkame a gidan yari biyo bayan wata mumunar zanga-zangarkungiyar dalibai taranar 19 ga watan Oktoban da ya gabata wace tayi sanadiyar konekonen motoci da fashe-fashen madubai a titunan birnin Yamai .
Sakamakon binciken da kotu ta gudanar bayan sauraren wadanan dalibai da ma’ikantan birnin Yamai suka zarga da laifin tada zaune tsaye da haddasawa jama’ar da ba su ji ba su gani ba asarar dukiyoyinsu a yayin zanga zangar da kungiyar USN ta dalibai ta shirya da nufin neman a magance masu matsalolin da suka hada da rashin wadatattun dakunan karatu da bencina da karancin malamai. Alkalin ya dauki matakin sallamar dalibai 27 daga cikin 31 da suka shafe makwanni 3 a gidan kaso yayin da sauran 4 suka samu sakin talala to sai dai wannan mataki ya zamewakungiyar dalibai ta USN abinda bahaushe ke cewa ga koshi ga kwanan yunwa inji shugabanta USAINI SAMBO USMAN .
Su ma iyayen daliban da kotu ta sallama sun yi farin ciki da wannan mataki ganin yadda ya kawo karshen kai da kawon da suka yi fama da shi tsakanin gida da mashara’anta zuwa gidan yari a tsawon Kwanaki fiye da 20.
Ga karin bayani.