Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijar Ya Sa Hannu Kan Dokar Hana Kulle Dan Jarida


Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Shugaban Nijar ya sa hannu akan dokar da ta hana kulle dan jarida idan dai yana aikinsa ne kain da nain.

A jamhuriyar Nijar kungiyoyin ‘yan jarida da na fararen hula sun yi ALLAH wadai da yadda ake gallazawa ‘yan jaridaa yayin farautar labaru kamar yadda a ranar da ake tarben tsohon kakakin majalisar dokokin kasa HAMA AMADU jami’an tsaro suka tsare wasu ‘yan jarida masu zaman kansuyayinda anasu bangare masu zanga zanga suka bubugi wasu ‘yan jarida.

Lamari na baya bayan nan shine wanda ya wakana a ranar Asabar din da ta gabata a yayinda ake artabu tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan Hamma Amadu inda ‘yan jarida suka huskanci muzgunawadaga bangarorin biyu abinda tsohon shugaban cibiyar ‘yan jarida maison de la presse BOUBAKAR DIALLO yace an taka doka fiye da kima.

Kamar yadda ‘yan magana ke cewa dillalin wada shi ya san kudin dan jariri dalili kenan da kungiyoyin fafitikar kare hakkin jama’a suka fara nuna damuwa akan halin haula’in da aikin jarida ke kan hanyar fadawa. SIRAJI ISA shine shugaban MOJEN.

A nasu bangare hukumomin kasar Nijar na ganin wuce gona da iri daga wasu ‘yan jarida a yayin neman bayanai shi ke ingiza jami’an tsaro cafke su.

Abin tuni a farkon darewar kan sa karagar mulkin Niaer shugaba ISUHU MAHAMADU ya saka hannu akan takardar kawo karshen kulle dan jarida akan aikinsa sannan ya sha alwashin zama lauyan dukkan ‘yan jarida a wurin takwarorinsa na sauran kasashen duniya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG