Matsalar tsaro da ta bakin haure da matsalar canjin yanayi na kan gaba a yau a jerin matsalolin dake maida hannu agogo baya a aiyukan ci gaban kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa dalili kenan da kungiyar tarayyar turai ta ware miliyan hamsinna euro domin tallafawa kasar Nijer ta fuskanci wadanan matsaloli.
Kwamishinan kungiyar Tarayyar Turai M.MIMICA NOVEN ya ce « jami’anmu dake Bruselles a shirye suke su hada gwuiwa da Nijer domin tafiyar da aiyukan wannan shiri saboda haka muna jiran shawarwari na zahiri daga bangarenku dangane da bukatun wannan kasa a fannonin da shirin ya kunsa ta yadda zamu gaugauta fitarda wadanan kudade a fara aiki akan lokacin da aka tsayar kamar yadda matemakina ya alkawarta maku a ziyarar da ya kawowa Nijer a watan Satumban da ya gabata ».
Kungiyar ta Tarayyar Turai ta kara kebe wasu kudaden na daban domin fannin walwalar al’umma.
Kwamishinanmai kula da huldar kasa da kasa da ci gaba yace
« Jama’a maza da mmata dake wurin wannan buki ina mai farin ciki saka hannu akan wannan yarjejeniya da ta kunshi milyan 36 na dalar euro domin karfafa aiyukan kiwon lafiyar al’umar Nijer musamman mata da yara kanana da aiyukan bayar da ilimi ga ‘yan mata.
Ministar harakokin wajen jamhuriyar Nijer Madame KANE AISHATU BULAMA ta bayyana cewa tuni kasar ta shirya wata tawagar manyan jami’an da su halarci taron da kasashen duniya ke shirin gudanar wa a birnin LA VALETTE kan batun bakin haure daga ranakun 11 da 12 ga watan nan na Nowamba .
Ga karin bayani.