Cikin wani yanayi na kila wa kala ne bangaran na ABDU LABO ya soma wannan taron congres sanadiyar matakin haramcin da alkali ya dauka da farkobiyo bayan karar da tsohon shugaban kasa ALHAJI MAHAMAN USMAN ya shigar to amma daga bisani kotun daukaka kara ta bada iziningudanar da taron kamar yadda dan takarar da aka tsayardomin neman shuganbancin NijarministaABDU LABO ya bayyana.
Sai dai masu rajin kare demokradiya irin su ALHAJI SALISU AMADU na kungiyar Sauvons le Niger na ganin bangaran na LABO bai mutunta tsarin shara’a ba.
Minista ABDU LABO ya zauna gidan kasoa watannin baya saboda zarginsa da hannu a harakar sayan jarirai kafin daga bisani a bada bailinsa saboda haka na tambayeshi shin ba ya ganin wannan zai kawo cikas ga takararsa ?
Ya zuwa yanzu bangaran tsohon shugaban kasa Mahaman Usman bai ce komai ba akan wannan sabon mataki yayinda ABDU LABO da makardabansa suka fara kiraye kirayen a hada kai a fidda jam’iyyar CDS RAHAMA a zabubukan da za’a yi a shekara mai zuwa.
Ga karin bayani.