NIJAR: Ana Wayar Da Kan Jama'a Kan Zagaye Na Biyu Na Zabe

Hukumar CENI ta Nijar

Hukumar CENI ta Nijar

Kungiyoyin rajin kare dimokradiya sun kaddamar da ayyukan fadakar da jama’a tare da tunatar da masu hannu akan sha’anin gudanar da zabe

Yayinda shirye shiryen zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 21 ga watan nan na Fabreru suka kankama kungiyoyin rajin kare dimokradiya sun tunatar da al'umma akan batun mutunta dokokin zabe don ganin komai ya gudana cikin kyakkyawan yanayi.

Ganin irin abubuwan da suka wakana a yayin zabubukan da aka gudanar a ranar 27 ga watan disamban 2020 ne ya sa kungiyar fafatika ta MPCR da hadin guiwar wasu fitatun masanan doka irinsu Pr. Djibril Abarchi na jami’ar Yamai kaddamar da ayyukan fadakar da jama’a game da wasu mahimman dokokin zabe da zasu taimaka a gudanar da zagaye na biyu na ranar 21 ga watan fabreru cikin kyaukyawan yanayi haka kuma masanan na ganin bukatar ankarar da kotun tsarin mulkin kasa kanta game da wasu kura kuran dake gurbatar da zabe.

Taron mahawarar MPCR ya gano cewa wajibi ne a nan gaba kotun tsarin mulkin kasa ta aika wakilai a wuraren da ake korafin an aikata ba daidai ba a yayin gudanar da zabe domin tantancewa kanta gaskiyar lamari.

‘yan siyasar da suka halarci wannan zama sun yaba da yunkurin:

Hadin guiwar na MPCR da masanan doka ya jaddada aniyar ci gaba da shirya irin wannan mahawarar bainar jama’a a Yamai da sauran yankunan Nijer har zuwa lokacin da za a bayyana sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da zai hada Mahaman Ousman na RDR Canji ta kawancen hamayya wato CAP 20 21 da Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya ta kawancen Coalition Bazoum 2021.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Mahawarar Bainar Jama'a Akan Dokokin Zabe