“Da misalin karfe 12 na rana aka kai harin kuma an samu mace-mace, abinda wani babban jami’i a yankin ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP kenan, ba tare da ya bada adadin wadanda harin ya shafa ba ko cikakken bayani akan farmakin.
Haka kuma wani jami’i shi ma ya ce an kashe farar hula da yawa a wani harin da aka kai a Tchamo-Bangou, wani kauye da ke kusa da iyakar kasar da Mali.
“Maharan sun je su zagaye kauyen ne suka kuma kashe har mutane 50. An kai wadanda suka jikkata asibitin gundumar Ouallam, a cewar wani dan jaridar gidan rediyon yankin wanda ya so a sakaya sunansa.”
Harin dai ya faru ne a ranar da aka fidda sakamakon zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka yi a Nijar wanda ya nuna cewa dan takarar jam’iyya mai mulki Mohamed Bazoum shi ne ke kan gaba, yayin da kuma ake shirin yin zabe zagaye na biyu a wata mai zuwa.