A ranar Litinin 4 ga watan Oktoba Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Nijar da hukumomin kasar ta Nijar sun yi addu’oin tunawa da wasu sojan Nijar 4 da takwarorinsu 4 na Amurka wadanda suka rasu sakamakon harin ta’addancin da ya rutsa da su a kusa da kauyen Tongo-Tongo na jihar Tilabery.
A ranar 4 ga watan oktoban 2017 akai kai dakarun kasashen biyu hari.
Shekaru 4 bayan faruwar wannan al’mari gwamnatocin kasashen 2 na ci gaba da jinjinawa wadanan gwarazan dakaru.
Mataimakiyar jakadan Amurka a Jamhuriyar Nijar Mme N’garnim Susan ta jagoranci taron inda ta jinjinawa dakarun.
Ta kara da cewa shekara 4 kenan da “muke alhinin rasuwar wadanan askarawa bayan da suka yi babban gumurzu da ‘yan ta’adda masu dimbin yawa a kauyen Tongo-Tongo.”
Jajircewar da wadanan sojoji suka nuna a yayin wannan kafsawa da ‘yan ta’addan da suka yi masu kwanton bauna alama ce da ta nuna yadda sojan na Amurka da na Nijer suka nuna jarumtaka saboda haka gwamantocin kasahen 2 ke alfahari da su inji Malan Achirou Goudia jami’in kula da harakokin sadarwa a ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Nijar.
Ministan tsaro Alkassoum Indatou da karamin ministan cikin gida da shugabanin runduna mayakan sojan Nijer sun halarci wannan taron addu’oi.
General Iro Oumarou shine babban hafsan dake bai wa shugaban kasa shawara akan sha’anin tsaro shi ma ya yi jinjina irin gagarumar gudunmowa da sojojin suka mayar.
Kasar Amurka na kan gaba a jerin kasashen da ke tallafawa Nijar a fannin tsaro, abin da ke kara karfafa huldar kasashen 2 masu manufa daya akan batun yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Harin Tongo-Tongo wanda ya haddasa zullumi a wajen al’uma wani abu ne da ya zo da daurin kai sosai a bisa la’akkari da yadda alamu ke nunin an kitsa shi ne da hadin kan wasu daga cikin mazaunan karkarar da ake kokarin samarwa tsaro.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5