Ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa dakarun tsaron kasar sun samu nasarori sosai, a rawar dajin da suka kaddamar a farkon watan nan na Fabarairu, da hadin gwiwar sojojin rundunar Barkhane a Arewacin yankin Tilabery, a iyakar Mali da Nijar, inda suka hallaka ‘yan ta’adda sama da 100 tare da kama tarin makamai da babura.
Tun a ranar 1 ga watan Fabarairu ne sojojin Nijar da takwarorinsu na Faransa, suka kai wani farmaki a Arewacin yankin Tilabery, da kan iyakar Mali da Nijar abinda ya basu damar hallaka ‘yan ta’adda kimanin 120.
'Yan ta'adda 23 daga cikinsu, sun fada tarko sojojin hadin gwiwar ne a kauyukan Inates, Tongo-Tongo, da Tiloa inji sanarwar ma’aikatar tsaro. Wacce ta kara da cewa dakarun sun kama babura 10, hade da wasu kayayyakin hada boma-bomai. Wani dan jam’iyya mai mulki Assoumana Mahamadou, ya bayyana farin cikinsa da jin wannan labarin.
A ra'ayin wani dan adawa Ibrahima Diakite, canjin shugabancin da aka samar a rundunar mayakan kasar Nijar a tsakiyar watan jiya ne ya fara bayar da irin wannan kyakkyawan sakamakon.
Kasar Faransa wacce ta girke dubban sojoji da sunan yaki da ta’addanci a yankin Sahel, ta sha suka daga jami’an fafutika a kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso a watannin baya.
Saboda zargin cewa ba sa tabuka wani abin a zo a gani. Abinda ya sa jami’in fafutika Salissou Amadou ya ce wannan gwagwarmayar ce ta fara tasiri a wajen hukumomin Faransa.
A yanzu dai ‘yan kasa sun zuba ido don ganin irin abubuwan da bincike a ma’aikatar tsaron Nijar ya gano, game da dalilan da ake zargin sune suka hana ruwa gudu a yakin, da Nijer ta kaddamar kan kungiyoyin ta'addancin Mali.
A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Facebook Forum