Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Dakarun Amurka Suka Kubutar Da Dan Kasarsu Da Aka Yi Garkuwa Da Shi a Najeriya


Wasu dakarun Amurka yayin akin zaman Lafita da sake yi a Afghanistan, ranar 7 ga watan Agusta, 7 2018.
Wasu dakarun Amurka yayin akin zaman Lafita da sake yi a Afghanistan, ranar 7 ga watan Agusta, 7 2018.

Rahotanni daga birnin N’Konni a Jamhuriyar Nijar na cewa, wani Ba’amurke da aka sace a kasar aka tsallaka da shi arewacin Najeriya ya samu kubuta.

Rahotanni daga birnin N’Konni a Jamhuriyar Nijar na cewa, wani Ba’amurke da aka sace a kasar aka tsallaka da shi Najeriya ya samu kubuta.

Kwanaki hudu da suka gabata wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne suka sace Ba’amurken a garin Massallata a Gundumar birnin N’Konni suka kuma tsallaka da shi Najeriya da ke makwabtaka da yankin.

Garin Massalata na da tazarar tafiyar kilomita 400 gabas ga babban birnin Yamai.

Wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon Jonathan Hoffman ya fitar, ta ce da sanyin safiyar yau Asabar dakarun Amurka suka kwato mutumin, amma sanarwar ba ta ambaci sunansa.

“Dakarun Amurka sun gudanar da wani farmaki da sanyin safiyar ranar 31 ga watan Oktoba a arewacin Najeriya don kubutar da wani Ba’amurke da wasu ‘yan bindiga suka sace.” Sanarwar ta ce.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ba’amurken yana cikin koshin lafiya yana kuma karkashin kulawar ma’aikatar harkokin wajen Amurka. Kuma babu wani sojan Amurka da ya ji rauni a lokacin wannan farmaki.”

Hoffman ya kuma nuna godiya ga “kawayenmu na kasa da kasa da suka mara mana baya wajen gudanar da wannan aiki.”

“Amurka za ta ci gaba da kare al’umarta da kuma muradunta a ko ina a duniya.” In ji Hoffman

Ko da yake sanarwar ba ta ambaci mutumin da aka kubutar ba, amma wakilin Muryar Amurka Harouna Mamane Bako da ke yankin birnin N’Konni ya zanta da mahaifin mutumin mai suna Bruce Walten wanda ya tabbatar mai da cewa lallai an kubutar da dansa

“Offishin jakadancin Amurka a Yamai ya sanar da ni cewa ya samu kubuta.” Walten ya fada ta wayar tarho.

Da aka tambayi Walten yadda yake ji bayan kubutar da dansa sai ya ce “ai babu kamar wannan rana mai dadi tun da dana ya kubuta.”

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato sunan Ba'amurken a matsayin Philip Walton.

A lokacin hada wannan rahoto jirgin Amurka mai saukar ungulu da ke dauke da Ba’amurken mai suna Peter Walten na gab da sauka a Yamai, bayan da a ka kubutar da shi daga hannun wadanda suka yi garkuwar da shi.

Jamhuriyar ta Nijar wacce ke yankin yammcin Afirka ta sha fama da matsalolin tsaro da suka hada da na mayakan Boko Haram da na ISWAP tana kuma da iyaka da Najeriya da ita ma ke fama da makamantan wadannan matsaloli na tsaro da suka hada har da na masu satar mutane don neman kudin fansa.

Ba'amurken kan yi kiwon rakuma da awakai tare da shukar mangoro a kusa da kan iyakar kasar ta Najeriya.

Wasu mutane shida ne suka far masa da bindiga kirar AK -47 akan babura a gidansa da ke kauyen Massalata na a kudancin Jamhuriyar Nijar a ranar Talata suka sace shi.

A watan Agustan da ya gabata wasu ‘yan bindiga akan babura suka halaka wasu ‘yan kasar Faransa shida da wani dan kasar ta Nijar a yankin Tillaberi.

A kuma shekarar 2017, wasu mayaka masu ikrarin jihadi suka kashe wasu sojojin Amurka hudu a yankin Tongo Tongo a Jamhuriyar ta Nijar da wasu ‘yan kasar ta Nijar su biyar da ke musu rakiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG