Cikin asibitocin da suka anfana da tallafin magunguna sun hada da Asibitin Peace mai zaman kasa da asibitin kwararru da cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dukansu a birnin Yola.
Shugaban ma'aikata na jihar Adamawa Malam Musa Kaibo wanda ya amshi magungunan a madadin gwamnatin jihar kana ya mikawa shugabannin asibitocin ya yi bayanin dalilin da ya sa asibiti mai zaman kansa ya ci gajiyar tallafin.
Yace gwamnatin Adamawa ta godewa asibitin. Kodayake asibiti ne na kudi amma shugabanta ya amince ya taimakawa wadanda rikici ya rutsa dasu ba tare da karbar ko kwandala ba. Saboda haka dole a gode masa. Gwamnatin jiha zata cigaba da tallafawa irinsu.
Tallafin na zuwa ne bayan harin kunar bakin wake da ya auku a tashar tifa ranar 17 ga wannan watan inda mutane sama da talatin suka yi asarar rayukansu.
Asibitin Peace mai zaman kansa inji daraktanshi Dr Niyi Oriolowo ya yiwa mutane fiye da hamsin da hare-haren Boko Haram ya raunata jinya kyauta. Daraktan yace aikin kiwon lafiya aikin taimako ne. Ko mutum nada kudi ko babu idan ya shiga damuwa dole a taimaka. Yace shi kansa dan talaka ne amma tunda Allah ya bashi abun taimako dole ne ya yi. Ya yiwa Allah godiya da ya taimakeshi domin shi ma ya taimaki wasu.
Babban sakataren hukumar kai doki mallakar jihar Adamawa Malam Haruna Furo yace duk da cewa mai asibitin ba dan asalin Adamawa ba ne amma taimakon da ya yi alama ce ta kishin kasa. A koyaushe aka kai masa mutane baya korafi ko da kudi ko babu. Da kudinshi yake sayen magunguna yana kula da mutane.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5