Wadanda suka jikata suna kwance a sibitoci cikin garin Yola inda ake yi masu jinya.
Bam din ya tashi ne a wani waje dake da hada-hadar jama'a a tashar 'yan tipa a jambutu bye pass. Wurin bashi da nisa da Masallacin Juma'a inda makonni biyu da suka gabata wani bam ya tashi.
Alhaji Sa'adu Bello jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA ya bayyana halin da ake ciki yanzu.
Lamarin ya faru ne yayin da gwamnan jihar ke ziyarar aiki da shugaban kasa a jihar Kebbi.Batun ya tada hankalin gwamnan. Gwamnan ya yanke ziyarar aikin da ya keyi da shugaban kasa zai koma Yola yau.
Gwamnan yace zai sadu da jami'an tsaro su kara daukan matakai amma ya gargadi jama'a da su daina taruwa a wuri daya. Su dinga lura da duk inda suke. Ya kira a cigaba da yin addu'a.
Ga karin bayani.