Jihar Adamawa na cikin daya daga cikin jihohin dake da dubban 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.
Jami'ar hukumar a Najeriya Angela Dikongo Atengana tace dole a hada hannu wajen tallafawa wadanda suka samu suka tsira da rayukansu. Suna bukatar a sake tsugunar dasu.
Jami'ar ta bayyana aniyar hukumar na samarda gidaje 200 ga iyalai dari biyu da rikicin Boko Haram ya daidaita na soma tabi a jihar Adamawa.
Tace sun kawo ziyarar ne saboda gani da ido irin halin da 'yan gudun hijiran suke ciki da kuma sanin irin tallafin da suke bukata. Tace akwai bukatar hada hannu domin a tallafawa jihar Adamawa wajen ginawa mutane muhalli. Tace abun da suke jira yanzu daga gwamnatin jihar shi ne ta nuna masu wurin da zasu soma aiki.
Tawagar ta kunshi wata fitarciyar mawakiya Onyeka Onwenu wadda ta bayyana mahimmancin taimakawa 'yan gudun hijiran.
Ita ma hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya tace a shirye take ta hada hannu da kungiyoyi daban daban da masu hannu da shuni.
Ita ma hukumar bada agaji ta jihar tace zata taimakawa mutanen wajen gyara masu gidaje ko kuma basu kudi su yi gyara. Zasu gyara asibitoci da makarantun da aka lalata.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.