Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Kudin da Gwamnati Ta Ranto Ya Haddasa Rikici a Majalisar Dokoki


Udara dingin dan gerimis tidak menghalangi para pengunjung untuk menikmati kilauan cahaya lampu, minuman anggur dan barang-barang hadiah liburan berwarna-warni di pasar Natal Berlin, 27 November 2017.
Udara dingin dan gerimis tidak menghalangi para pengunjung untuk menikmati kilauan cahaya lampu, minuman anggur dan barang-barang hadiah liburan berwarna-warni di pasar Natal Berlin, 27 November 2017.

Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Adamawa saboda kudin da jihar ta ranto wanda kuma wani dan majalisar yana son a binciki gwamnati kan yadda ta yi da kudin lamarin da ya kai ga dakatar dashi

Kakakin majalisar ya dakatar da dan majalisan dake kan gaba wajen binciken gwamnatin jihar kan yadda take kashe kudaden da ta ranto da kuma batun nera biliyan goma sha daya da gwamnatin ke son kashewa akan ayyukan da tun farko basa cikin kasafin kudi.

Dan majalisar da aka dakatar Abubakar Abdulrahaman wakilin mazabar Mubi ta Kudu yace manufar yunkurinsu shi ne a tabbatar da daidaito.Yace ya dauki alkawari zai yi wa jama'ar Adamawa aiki ba sani ba sabo. Shi amana ce aka dora mashi. Gwamna Bindow ba shi ne maigidansa ba ko kakakin majalisa.Talakawan Adamawa yake yiwa aiki.

Kakakin majalisar Kabiru Mijinyawa bayan ya dakatar da Abubakar Abdulrahaman na tsawon wata uku ya kuma rushe duk kwamitocin majalisar kana ya fitar da wani dan majalisar da suka kara da Abubakar Abdulrahaman daga zauren majalisar..

Onarebul Hassan Maiguma yace duk abubuwan dake faruwa a majalisar gyara ne saboda a kawar da halin 'yan tasha daga majalisar. Majalisa ba wurin taron 'yan tasha ba ne.

To saidai wasu na zargin cewa da hannun gwamnati a wannan takaddamar amma kwamishanan yada labarai na jihar ya musanta zargin .

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG