Gwamnatin jihar ta yi nazari akan abubuwan dake faruwa a jihar biyo bayan yawan hare-hare da suka faru da hasarar rayuka da dama.
Gwamnati ta gane 'yan ta'adan sukan kai hari ne wuraren da jama'a ke taruwa kaman masallatai da mijami'u ko kasuwa. Saboda haka gwamnati ta hana cin kasuwar dare. Masu shaguna da gidajen sayar da abinci ko shan giya dole su rufe shagunansu da karfe shida na yammar kowace rana.
Gwamnati ba zata bari a cigaba da kashe mutane 30 ko 50 kullum tare da raunatasu kullum ba.
Dangane da wadanda suka samu rauni a hare-haren da suka auku gwamnatin jihar ta dauki nauyin jinyarsu.
Tun farko dai kungiyoyi, shugabannin addini da na al'umma sun kira gwamnati da a sake lale ganin yadda hare-haren suke kara yawa.
Shaikh Bala Lau shugaban kungiyar IZALA ta Najeriya ya nuna takaicinsa da abubuwan dake faruwa. Abubuwan da suka faru a Yola da Kano masifu ne kuma ya yi addu'ar Allah Ya Kawo karshen aika-aikar. Amma Shaikh Lau yace babbar mafita ita ce komawa ga Allah. Ya kira gwamnati ta sake tashi ta sa ido da daukan duk matakan da suka kamata domin tabbatar da zaman lafiya.
Tuni dai Shugaba Buhari ya yi tur da hare-haren Yola da Kano. Shugaban ya nuna takaicinsa da juyayinsa akan wadannan munanan hare-hare. Ya jajantawa wadanda abun ya shafa da kira a yi hattara domin aikin tsaro na kowa da kowa ne.
Ga karin bayani