Malam Halilu Muhammad shi ne manajan cibiyar samarda ingantacen ruwan sha a yankunan karkara da kuma tsaftace muhalli na jihar Adamawa yace an samu koma baya.
Koma bayan ya faru ne sakamakon kasawar gwamnatin Adamawa na biyan kashi 30 bisa 100 na asusun karo karo na hadin gwuiwa da kungiyoyin majalisar dinkin duniya.
Malam Muhammad yace lallai ba'a cimma muradun bada ingantacen ruwan sha da tsaftace muhalli ba a jihar Adamawa da ma wasu kasashen da yanzu suna son a kara wa'adi. Cikin shekaru bakwai da suka wuce Adamawa bata bada nata kason ba.
A wannan shekarar ce ta fara bada nata kason sannan kasashen waje suka soma bada nasu har ma sun gina rijiyoyin bututu 200 tare da mazagaya 40.
Jihar Adamawa na bukatar sama da nera miliyan 12 domin tara kayan zubar da shara da kuma motocin kwashe shara a fadar jihar da kuma kewaye. Kawo yanzu gwamnatin jihar bata mallaki gwangwanin shara ko motar kwashe shara daya ba.
Babu ingantacen ruwan sha kuma ba'a tsaftace gidajen bahaya dake kasuwaanni ko tashoshin motocin haya.
Ga karin bayani.