Adadin wadanda suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen a yammacin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya karu zuwa akalla 29 tare da gano akalla mutum 128 da suka tsira da rayukansu, wasu kuma ba a san adadinsu ba, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar a ranar Alhamis.
WASHINGTON, D. C. —
An kwashe kwanaki ana aikin ceto bayan kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji tsakanin 250 zuwa 300 ya kife a daren Lahadin da ta gabata a lokacin da ya afka cikin kututturen bishiya a karkashin ruwa a wani kogi a yankin Kutu.
"Daukar fasinjoji fiye da kima da tafiya cikin dare wanda ya saba wa ka'ida ana kallon shi ne a musabbabin wannan bala'i," in ji shugaban Kutu Jacques Nzeza ta wayar tarho.
Ya ce mutum 29 da aka sani sun mutu sun hada da mata 15 da yaro daya.
Shugaban wata kungiyar farar hula na yankin, Fidele Lizoringo, ya ce masunta sun kara gano wasu gawarwaki hudu na shawagi a cikin kogin amma ba su iya ceto su ba.
Lizoringo ya ce an yi rajistar mutum 152 da suka tsira.
-Reuters