Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Lakume Rayukan Mutane 9 A Zamfara


Hadarin kwale-kwale a Sokoto
Hadarin kwale-kwale a Sokoto

Masu aikin ceto a hatsarin Jirgin Ruwa da ya faru a kauyen Kali na Karamar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara, sun tabbatar da tsamo gawarwakin guda tara na mutanen da hatsarin Jirgin ruwa ya rutsa da su a yankin.

Lamarin dai ya faru ne sanadiyyar firgici da tashin hankalin da alummar suka shiga sakamakon samun labarin yunkurin 'yan bindiga na aukawa garin domin kai masu hari.

A hirar shi da Muryar Amurka, Aliyu Sukata Kali, Sarkin Jirgin Ruwa na yankin kuma matukin Jirgin da ya samu hatsarin ya bayyana yadda lamarin ya faru.

"Abunda ya faru shine, an ce barayi sun kawo kusa da garin mu, hakan yasa jama'a suke ta tururuwa suna barin barin garin inda muke fiton su da jirgin ruwa. Mun dauki sawu na biyar kusan mutun hamsin, mun kai tsakkiyar ruwa sai jirgin ya nutse"

Yace ganin hakan yasa suka yi kururuwa suna neman agajin al'umma, inda masu aikin ceto fiye da mutun Dari suka afka cikin ruwan wasu akan gora wasu akan masaki, wasu kuma suna kurma suka dinga ceto mutane har aka fitar da mutun arba'in yayin da aka samu gawarwakin mutane tara. Sai wani mutun daya da yanzu haka yake a asibiti, rai kwakwai-mutu-kwakwai.

Hadarin kwale-kwale a Jihar Taraba
Hadarin kwale-kwale a Jihar Taraba

Kasimu Umar, wani shedan gani da ido, kuma daya daga cikin wadanda suka yi aikin ceton mutanen, yace lokacin da lamarin ya faru sun yi gudu ne, suna kan tsauni domin tsira da rayukan su daga harin na barayin daji, kamar yadda su ka saba duk lokacin da suka ji samatar barayin. Ya ce,a wannan karon sun bar iyalan su da 'ya'yan su suna baya hakan yasa ba su wuce ba, su ka tsaya su jira isowar su.

Yace "Daya daga cikin mu da ya lura jirgin zai nutse, sai ya afka a cikin ruwan domin ya jawo iggiyar jirgin, amma kafin ya samu nasarar yin hakan sai jirgin ya nutse,kaya kawai ake gani a sama".

A nata bayanin, Malama Amina daya daga cikin wadanda aka ceto bayan nutsewar jirgin tace sun shiga rudani da tashin hankali a lokacin da jirgin ya nutse kafin a samu nasarar ceto su.

Tace sun shiga jirgin ne tare da yaranta biyar kuma an ceto su duka, yanzu haka suna karbar magani a wani asibiti dake yankin.

Hadarin kwale-kwale a Jihar Taraba
Hadarin kwale-kwale a Jihar Taraba

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar Zamfara, kuma Dan Majalisar dake wakiltar yankin, Hon Adamu Aliyu Gummi , ya bayyana takaicin aukuwar lamarin, nan take ya kuma bada kudi domin sawo wadansu jiragen ruwan kasancewa wannan ce kadai hanyar da al'ummar ke iya fita garin.

Shi dai yankin na Kali da ke gundumar Birnin Magaji a Karamar Hukumar Gummi ta jihar Zamfara, yana daya daga cikin yankunan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, da lamarin ya daidaita su, bugu da kari, yankin na da matukar wahalar shiga saboda rashin hanya da kalubalen tsaro.

To Sai dai Allah ya albarkaci kauyen na Kali da makwaftan shi da albarkatun noma masu tarin yawa, da suka haka da Gero da Dawa da wake da Kwarya da Dankali da dai Sauran su. Suna kuma noma sau biyu a shekara, noman rani da na damina.

Saurari cikakken rahoton Abdulrazak Bello:

Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Lakume Rayukan Mutane 9 A Zamfara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG