Muna So Mulki Ya Koma Hannun Farar Hula – ‘Yan adawa a Gabon

Mutane a titunan birnin Libreville, Gabon

Babbar kungiyar ‘yan adawar kasar Gabon, Alternance 2023, ta yi kira ga kasashen duniya a yau Juma'a da su karfafa wa gwamnatin mulkin da ta hambarar da shugaba Ali Bongo kwarin gwiwar ta mika mulki ga farar hula.

Gabon

WASHINGTON, D.C. - Jami’an soji sun kwace mulki ne a wani juyin mulki a ranar Laraba ‘yan mintoci bayan sanar da Bongo a matsayin wanda ya lashe zabe a karo na uku.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon

Sun tsare shi a cikin gida sannan suka zabi Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban rikon kwarya.

Gwamnatin mulkin sojan dai ba ta ce komai ba game da shirinta na kai tsaye bayan kawo karshen mulkin zuri’ar Bongo na kusan shekaru sittin da suka yi a kan karagar mulki.

Matakin sojin ya sa jama'a sun bazama kan titunan Libreville suna nuna farin cikinsu.

Tun a shekara ta 2009 Bongo ya karbi mulki a kasar daga hannun mahaifinsa lokacin da ya rasu bayan ya zama shugaban kasa tun a shekarar 1967.

Libreville, Gabon, Aug. 30, 2023.

Masu adawa da shi dai sun ce iyalin ba su yi wani abu ba wajen rabon arzikin man fetur da ma'adinai na Gabon ga al'ummar ta miliyan 2.3, wadanda kusan kashi uku na cikinsu ke fama da talauci.

"Mun yi farin ciki da aka hambarar da Ali Bongo amma muna fatan kasashen duniya za su tashi tsaye don tabbatar da jamhuriya da tsarin dimokuradiyya a Gabon ta hanyar neman sojoji su mayar da mulki ga farar hula," Alexandra Pangha mai magana da yawun shugaban Alternance 2023 Albert Ondo Ossa, ya fadawa BBC.

Alternance 2023 ta ce tana son a sake kirga kuri’u gaba daya a zaben na ranar Talata wanda ta ce zai nuna Ondo Ossa ne ya lashe zaben.

Jenerali Brice Oligui Nguema, Agosti 16, 2023. Picha na AFP.

Hukumar zaben Gabon ta ce an sake zaben Bongo da kashi 64% na kuri’un da aka kada, yayin da Ondo Ossa ya samu kusan kashi 31%.

Pangha ya ce 'yan adawa na fatan samun goron gayyata daga gwamnatin mulkin soji domin tattaunawa kan shirin mika mulkin kasar da ke Afirka ta tsakiya da kuma komawa ga tsarin jamhuriya amma ya ce har yanzu ba su samu komai ba.

A ranar Litinin ne ake sa ran za a rantsar da Nguema, shugaban jami’an da suka yi juyin mulkin, a matsayin shugaban rikon kwarya, kamar yadda gwamnatin mulkin soji ta bayyana. Zai kuma yi jawabinsa na farko na shugaban kasa a lokacin.

Wani hoto daga bidiyo na Janar Brice Clothaire Oligui Nguema, mutane sun daga shi sama a tinin birnin Libreville, Gabon, Aug. 30, 2023. (Gabon24 via AP)

Pangha ya ce "Muna ganin wauta ce su yi rantsuwa a ranar Litinin."

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka ya bukaci a ranar Alhamis din da ta gabata cewa sojoji su guji yin katsalandan a harkokin siyasa tare da yin kira da a gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Kasar Faransa da ta mulki kasar ta Gabon da kuma wasu kasashen yammacin turai sun yi Allah wadai da mamayar da sojojin suka yi.

-Reuters