Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juyin Mulkin Gabon Ba Zai Zama Na Karshe Ba A Nahiyar Afirka – Hasashen Masu Sharhi


Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon
Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon

A cewar mai sharhi kan al’amuran siyasa, Rotimi Olawale, juyin mulki na bazuwa a nahiyar Afirka ne saboda masu rike da madafun iko sun gaza wajen tabbatar da wanzuwar tsarin dimokardiyya mai inganci.

Najeriya ta bi sahun wasu kasashen nahiyar Afirka wajen yin Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a kasar Gabon.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda ke jagorantar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS, ya ce yana aiki tare da shugabannin kasashen duniya da kungiyar Tarayyar Afirka ta AU don ganin an sasanta rikicin siyasar Gabon da Nijar, inda sojoji suka yi juyin mulki.

Kakakin shugaban Najeriya Ajuri Ngelale ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da bibiyar al’amuran da ke faruwa tare da nuna matukar damuwa kan rikicin siyasar na Gabon.

A cewar Ngelale, Tinubu ya kuma damu da yadda juye-juyen mulki a nahiyar ke fadada, kuma yana aiki tare da sauran shugabannin kasashen nahiyar domin neman maslaha.

A ranar Laraba wasu manyan sojojin kasar Gabon suka kifar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba jim kadan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a makon jiya wanda ke cike da rudani.

Yanzu haka shugaban na Gabon na karkashin daurin talala a gidansa.

A wani hoton bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, an ga Bongo yana kira ga kawayen kasar ta Gabon da su fito su kalubalanci tsige shi da sojojin suka yi daga karagar mulki.

Sojojin juyin mulkin har ila yau sun sanar da soke sakamakon zaben da aka yi tare da rusa dukkanin madafun iko da ke gudana karkashin tsarin Dimokradiyya – kazalika sun rufe kan iyakokin kasar.

“Iko na mulki a hannun al’umar nahiyar Afirka yake ba hannun masu dauke da makamai ba. Shugaba Tinubu ya ce bai kamata a yi watsi da tsarin doka da ke gudana karkashin kundin tsarin mulki idan ana neman maslaha kan wata matsala a wannan nahiya tamu ba.” In ji Ngelale.

Wannan juyin mulki na Gabon shi ne takwas da aka yi a Afirka tun daga watan Agustan 2020, ya kuma faru ne wata guda bayan wani juyin mulkin da kungiyar ta ECOWAS da Tinubu ke jagoranta ke fadi-tashin ganin ta sasanta a Nijar.

Juyin mulki na Gabon har ila yau, wanda kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah-wadai da shi, na ci gaba da haifar da fargaba kan yadda tsarin bin doka da oda ke dakushewa a nahiyar.

A cewar mai sharhi kan al’amuran siyasa Rotimi Olawale da ke zaune a Abuja babban birnin Najeriya, juyin mulki na bazuwa a nahiyar ta Afirka ne saboda masu rike da madafun iko sun gaza wajen wanzuwar tsarin dimokardiyya mai inganci.

“Duk da cewa kungiyoyi ECOWAS da AU sun yi maza suna yin Allah wadai da juye-juyen mulkin da ake yi, akwia bukatar su rika samun lokaci suna auna yadda tsarin na dimokardiyya ke tafiya a nahiyar. Idan ba ya tafiya daidai, sai nemi wata hanyar shugabanci mafi a’ala da za ta kai su ga gaci. Kuma a hakikanin gaskiya, da yawansu ba da samar da abin da ake bukata.” Rotimi Olawale ya ce.

Emmanuel Njoku, shi ne Darektan kungiyar dabbaka tsarin Dimokradiyya da ke Abuja, a kuma tashi mahangar juyin mulkin da ake gani a nahiyar somin-tabi ne.

“Tsarin dimokaridiyya na fuskantar barazana a duk duk duniya. Amma a Afirka, irin yadda ake tafiyar da tsarin na dimokardiyya ta hanyar amfani da mulkin kama-karya, ban yi mamaki ba abin da ke faruwa ba, ba na kuma ganin wannan shi ne na karshe – za mu ga karin wasu juye-juyen mulkin.” Njoku ya ce.

A shekarar 2009 Ali Bongo ya karbi mulkin kasar ta Gabon daga mahaifinsa wanda ya mulki kasar tsawon shaker 42 kafin rasuwarsa.

Bongo ya kuma sauya kundin tsarin mulkin kasar don bai wa kansa damar neman wa’adi na uku.

A ranar Laraba, daruruwan mutane suka bazamaa kan titunan Libreville, babban birnin Gabon, suna farin cikin ganin karshen mulkin zuri’ar Bongo.

Njoku kenan yake cewa, “wannan fa kasa ce da ke da arzikin man fetur, amma al’umar kasar na fama da talauci. Idan ka kalli abin da kyau, tamkar an ‘yantar da alumar kasar ta Gabon ne daga wata zuri’a da ta kwashe tsawon lokacin tana mulki – kuma kada mu manta Ali Bongo na shirin dansa ya gaje shi idan ya tsufa.”

Yayin da kasashen duniya ke ta Allah wadai da hambarar da gwamnatin ta Bongo, dakarun juyin mulkin sun sanar da Janar Brice Nguema a matsayin sabon shugaban rikon kwarya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ta ce a ranar Litinin za a rantsar da Janar Brice.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG