Mun Kaddamar da Yaki Akan Ta'addanci - inji Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

​Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace gwamnati zatayi iya kokarinta domin mayarda dalibannan mata sama da 200 wajen iyayensu wadanda ‘yan Boko Haram suka sace a watan da ya wuce.
A jawabin da yayi wanda aka fitar Alhamis dinnan, Mr. Jonathan ya bayyana cewa yau kwanaki 45 kennan da faruwar wannan ta’asa. Ya kuma bayyana alhininshi ga iyalan yaran.

Shugaban yayi alkawarin kaddamar da yaki akan ta’addanci, kuma yace ya baiwa jami’an tsaron kasa umarni akan suyi amfani da duk wata hanya da doka ta tanadar domin kawo karshen yadda ‘yan ta’adda a Najeriya suke cin karensu babu babbaka.

Mr. Jonathan ya furta wadannan maganganun ne a jawabinsa na ranar Demokradiyya, ranar da aka ware ta domin hutu a kasa baki daya. Yace gwamnatinshi na maraba da hawa kan teburin shawarwari da ‘yan kasa wadanda suka taimakawa al-Qaida da wasu kungiyoyi masu nasaba da ita, idan har sukayi Allah wadai da ta’addanci.

Amma a yau Alhamis ne kuma, rahotanni sunce wasu ‘yan bindiga akan babura sun kashe a kalla mutane 32 a wasu kauyuka dake Jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.