Nan da nan dai babu wanda ya fito ya dauki alhkain kai harin.
Tagwayen harin bama bamai da aka kai a Jos din ranar talata data shige, sun halaka mutane 130. An aza laifin hare haren kan kungiyar Boko Haram. Kungiyar ta dauki alhakin sace ‘yan mata ‘yan makaranta su fiyeda dari uku, haka kuma ana dorawa kungiyar laifin kashe dubban mutane.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da gwamnatinsa suna fuskantar fushin ‘yan kasar da kuma sauran duniya domin kasa kubutadda ‘yan matan.
Ga 'yar tattaunawar da Halima Djimrao tayi da wakiliyar Sashen Hausa A Jos Zainab Babaji.