Wannan kiran ya zo ne daidai lokacin da majalisar dattawan Najeriya ta amince da sabunta dokar ta baci karo na uku a jihohin Adamawa, Borno, da Yobe wadanda a yanzu ma ana samun matsalar kai hare-hare a wasu kauyuka musamman a jihar Borno.Kwana kwanan nan aka kai hari a garin Alagardo inda aka hallaka mutane da dama aka kuma kone garin.
Alhaji Maidugu Aliyu tsohon dan jarida mai zaman kansa yanzu yace kira ne ga shugaban kasa da ya gaggauta nada kotun soji ya binciki rade-radi da jita-jita cewa su manyan sojoji basa ba na kasa da su umurnin mai da martani duk lokacin da 'yan bindiga suka kai hari wani wuri ko a wani gari ko kuma idan an ga 'yan Boko Haram zasu kai hari wani wuri.Yayi misali da garin Ngala inda ana ganin 'yan Boko Haram amma shugaban soji ya ki bada umurni a gama da su. A garin Sawa shugaban sojoji ya ki ya bada umurni a kama 'yan Boko Haram da suka shiga garin. Ya kira shugaban kasa ya bincika, menene matsalar yaran.
Alhaji Muhammed Bashir Talbari jami'in hanyar sadarwa ta zamani na gwamnan jihar Borno ya kira shugabannin sojoji da su ajiye aikinsu ko kuma shi shugaban kasa ya ajiye aikinsa. Duk lokacin da aka kai hari sai jami'an tsaro su fito suna musantawa. Hakan bai kamata ba. Yakamata su ji tsoron Allah.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.