Ya bayana haka ne a wata hira da suka yi da wakilin muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz, inda yake cewa alfanu shine za’a binciki duk kadarorinsu da na wadanda suke basu kudade,da suke aiwatar da wannan mugun aiki.
Yace”idan da gaske sukeyi ya zaman cewa za’a bi shuwagabanin kungiyoyi nan zuwa koina a bisu a kama sannan abi kudaden su a kowane banki a Najeriya da waje a narkar dasu, inda anyi haka muna ganin wannan zai kawo saukin rashin tsaron.”
Dr. Amuga Namala, ya kara da cewa wani abunda yake bukatar bincike shine zargin da akeyi na cewa akwai hannun wasu manyan jami’an tsaron Najeriya, a wannan batu na ‘yan Boko Haram, Yace” labaran da muke ji da abunda muke karantawa da abunda muke gani da idon mu shine akwai hadin baki na wasu manyan sojojin.”
Yayi kira ga shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda yace yana gani kamar abubuwa suna neman tabarbare masa da ya tashe tsaye yayi tunanin yanda za’a kawo karshen wannan abun batare da jin tsoro ko kuma neman kare kuriyasa ba.